20/09/2026
INALILLAHI WOINA ILAHIM RAJUNA 💔ðŸ˜
Rashin Hankali: Dr. Daud Gambo Ya Rasu A Hatsari Yayin Da Ya K**a Hanyar Jana'izar Mahaifiyarsa
A yau Dr. Daud Gambo ya sanar da mu rasuwar mahaifiyarsa, a yau ya k**a hanya zai je a yi jana'izar da ita sai kuma Allah Ya kaddara ya yi hatsari a hanya kuma nan take ya rasu. Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un!
Wannan bawan Allah likita ne kuma mai kishin addini da son jama'a! Ya rasu ba wasiya, ba sanarwa, ba shiri. Babun ta yi yawa. Ashe ranar rasuwarsa da mahaifiyarsa daya ne bai sani ba!
Allah Ya gafarta wa Dr. Daud Gambo da mahaifiyarsa, Ya jikansu, Ya haskaka makwancinsu, Ya sanya Aljanna ce makomarsu.
Marigayi Dr. Daud Gambo likita ne mai son jama'a da kishin addini, masoyin malamai da dalibai. Masoyin Professor Mansur Isa Yelwa da Professor Bashir Aliyu Umar, OON da Dr. Muhammad Kabir Haruna da Professor Isa Ali Pantami da sauran malamai. Mutum ne mai yada karatun malamai na Sunnah da na sauran huffazan Qur'ani, mai ladabi da karamci da kyakkyawar mu'amala.
Darasi: Jama'a mu kula, duniyar da muke cikinta tana cike da abubuwa, zaman duniya kawai abin tsoro ne ga dukkan mai rabon shiriya! Wannan labari ya koyar da mu cewa ajali na kusa, baya jiran shiri. Mutum na cikin shirin jana'izar wani, shi kuma nasa ajalin ya zo. Ya k**ata mu kasance cikin tuba, wasiyya, da shirin komawa ga Allah a kowane lokaci.
Health Awareness: Hatsarin mota na daga cikin manyan musabbabin rasa rayuka kwatsam. Yana da muhimmanci a kula yayin tafiya - a yi taka-tsantsan, a guji gudu da wuce sauri, a tabbatar da lafiyar mota, a huta idan an gaji, a yi addu'a kafin tafiya. Kuma a rika rubuta wasiyya da shirya al'amuran iyali tun da wuri, domin mutuwa ba ta da lokaci.
Allah Ya gafarta wa Dr. Daud Gambo da mahaifiyarsa da sauran mamatanmu baki daya, Ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarsu, Ya ba iyalansu, abokansu da malamansa hakuri da juriya. An bukaci a sanya shi da mahaifiyarsa a addu'a. Amin.
Source: Alkalin bayan fage, Ahmad Usman Elnafaty | For Public Awareness Only
🩺 Dr Idris Muhammad | For Community Awareness Only