Rahman Yosuf

Rahman Yosuf 🇳🇬 Nigerian 🇶🇦 Living in Doha
📖 Hafiz Al-Qur’an | Student of Hadith
🩺 MBBS • 2020
🤍 Faith | Knowledge | Service St. Nurse

Ko kun san da hakan game da Kasar Yemen 🇾🇪 ?Yemen kasace mai dauke da mutane akalla fiye da miliyan arba'in (40).Sama da...
14/09/2026

Ko kun san da hakan game da Kasar Yemen 🇾🇪 ?

Yemen kasace mai dauke da mutane akalla fiye da miliyan arba'in (40).

Sama da Mutum dubu dari biyar (500,000) na yan kasar mayakan Houthi ne.

Wata kila kun taba gansu a labaran talabijin ko Internet, Sirara ne, a wani lokacin zaka kanesu suna tafiya a cikin hamada sanye da takalmin silipas ko kuma babu takalmi kwata-kwata, suna dauke da bindigogi masu sarrafa kansu ko kananan makamai masu harba bami na roka.

Sun samo sunane daga kalmar "Hutis" ne domin karrama jagoransu Hussein Badreddin al-Houthi. Ya mutu a fagen fama yana da shekaru 48 a shekarar 2004.

Yemen tana fama da yakin basasa (Civil war) na tsawon shekaru sama da 50 tun bayan yakin duniya na biyu (WWII), a ta bangare guda, 'yan Houthi da kuma Gomnatin adawa a daya bangaren, 'yan Yemen masu yi wa Saudi Arabiya hidima, (Saudi-backade government).

Yan adawan kasar wato Saudi-backed government suna taya Isra'ila da Amurka cimma manufofin su akan kasar.

———————————————————————
'Yan Houthi sune kadai Larabawan da s**a taba tsayawa tsayin daka domin 'yan uwansu na Falasdinu. Kuma su kadai ne Larabawan da ba su sayar da kansu ga Isra'ila da Amurka ba.

Ku tuna cewa 'yan Iran Farisawa ne?, Domin rage musu kima a kafafen yada labarai, sai turawan yamma su kirasu da yan tada kayar baya.

Shin ko kun manta cewa 'yan Pakistan 🇵🇰 mutane ne da s**a ki sayar da yancinsu ga Amurka?, shiyasa suke kiransu da yan ta'åddá.

Kun sanda cewa Larabawa zasu iyayin komai saboda Amurka?

Kun sanda cewa zasu iya bayarda duk wani taimoka ga Amurka domin ta yaki yan uwansu Larabawa idan ta bukaci hakan?

Sun bayar da taimoko ga Amurka wurin kifar da Gomnatin Muhammad gaddafi na Libya 🇱🇾 a 2011, sadam Hussein na Iraq 🇮🇶 2002 da Bashar Al-asad na Syria 🇸🇾 .

Koda yaushe suna bin Amurka sauda kafa don gar ta yakrsu.

Amma Larabawan Houthi sunki biyya ga muradun Isra'ila da Amurka kamar yadda Afghanistan ba su yi ba.

Su ma sun yi yaki da Amurka babu takalmi ko sanye da silipas... Kuma sun yi nasara.

Daukaka da girmamawa ga mayakan dake yaki babu takalmi.

⚠️ kada ka taba yadda cewa yan Iran, Pakistan, Iraq, yamen da Syria yan ta'addåne!!

Sun kirasu da yan tada kayar bayane kawai don sunki biyayya ga muradun su.

Gada ka yadda saboda Ban bancin akida ta Musulunci ka fara kallon dan uwanka Musulmi a matsayin dan Taàdda!!.

Akidar sa tashice kaima taka-takace, Allah ne mai gafarta lafuka!!

American president (Trump): Idan ka kalli Gaza, a yanzu haka kyakkyawar dangantaka tana gudana. Abin ya kasance mai ban ...
13/09/2026

American president (Trump): Idan ka kalli Gaza, a yanzu haka kyakkyawar dangantaka tana gudana. Abin ya kasance mai ban mamakin gaske.

Ina ji a raina Amurka da Israela munyi babban aikin da za,a yabamu a Gaza.

Trump: Yarima mai jiran gado abokina ne na gari, kuma komai zai daidaita.
12/09/2026

Trump: Yarima mai jiran gado abokina ne na gari, kuma komai zai daidaita.

Shekaru 25 bayan hare-haren 11 ga Satumba, yaƙe-yaƙen da Amurka ke jagoranta sun kashe miliyoyin mutane, sun raba dubun-...
11/09/2026

Shekaru 25 bayan hare-haren 11 ga Satumba, yaƙe-yaƙen da Amurka ke jagoranta sun kashe miliyoyin mutane, sun raba dubun-dubatar miliyoyin mutane da muhallansu, sannan sun lakume tiriliyoyin daloli.

Ga alkaluman asarar rayuka da jikkata da aka samu sakamakon 'Yaƙi da Ta'addanci' da ma bayansa

📸 Al Jazeera English ✍️

Shugaban ƙasar Iran na wancan lokacin Seyed Ali Khamenei (Hagu) tare da shugaban Libya Muammar Gaddafi (Dama), su na gai...
10/09/2026

Shugaban ƙasar Iran na wancan lokacin Seyed Ali Khamenei (Hagu) tare da shugaban Libya Muammar Gaddafi (Dama), su na gaisawa a lokacin taron koli na 8 na ƙungiyar (Non-Aligned Movement) a shekarar 1986 a Harare, Zimbabwe. (Allah ya jikansu da rahamarsa Amen).

Muhammad Cisse ✍️

Wanda ya kafa kasar Pakistan, Muhammad Ali Jinnah tare da babban mataimakin gwamna (Viceroy) na karshe a Indiya, Lord Lo...
10/09/2026

Wanda ya kafa kasar Pakistan, Muhammad Ali Jinnah tare da babban mataimakin gwamna (Viceroy) na karshe a Indiya, Lord Louis Mountbatten da matarsa Edwina Mountbatten a 1947.

An dauki wannan hoton a ranar, 14 ga watan Agusta, a dai-dai lokacin da al'ummar kasar Pakistan suke bikin tunawa da samun ‘yancinsu (Ranar ‘Yanci) daga mulkin mallaka na Birtaniya. (1947) An kafa yankin kasar Pakistan mai ‘yanci bayan rabon kasar Indiya ta Birtaniya zuwa manyan kasashe biyu masu ‘yanci, wato Indiya da Pakistan.

Kunga irin abin da muke gaya muku a koda yaushe ko?👇🏻Waɗannan yaran da kuke gani ’ya’yan shahararren mawakin nan ne NAIR...
09/09/2026

Kunga irin abin da muke gaya muku a koda yaushe ko?👇🏻

Waɗannan yaran da kuke gani ’ya’yan shahararren mawakin nan ne NAIRA MARLEY bincike ya nuna cewa sun kasance yara masu tarbiyya da kuma kula da karatun addini. Idan kana bibiyarsu a TikTok za kaga irin yadda suke rera karatun Alƙur’ani mai girma sun shiga musabaƙu da dama.

Ba sai nayi wani dogon bayani ba. Kunsan cewa wannan tarbiyyar uwarsu ce ba wai ta mahaifinsu ba. Domin shi yana can yana yawon shows ɗinsa wataƙila ba zai san wacce irin hanya aka ɗora yaran ba amma dai yasan wacce irin uwa suke da ita.

Wallahi tallahi kada ka yarda kayi kuskuren auren macen da bata da ilimin Musulunci. Idan ba haka ba zaka iya jawo wa kanka da kuma ’ya’yanka matsala.

Mutum irin Naira Marley ma ya auri mace mai tarbiyya da addini ballantana kai. Ko da yake mutum yana iya yin kuskure a rayuwa samun mace ta gari a matsayin uwa ga ’ya’yanka babban nasara ne.

Shawara ta rage ga mai shiga rijiya.😌

Gomnatin Amurka na ci gaba da sauya manufofinta akan yaki da kasar IRAN!!!!Shin kodai Amurka mafita take nema?Meye raayi...
08/09/2026

Gomnatin Amurka na ci gaba da sauya manufofinta akan yaki da kasar IRAN!!!!

Shin kodai Amurka mafita take nema?
Meye raayinku akan wan nan?

Shugabannin Larabawa sun yi taro a birnin Alkahira a watan Satumba na shekarar 1970. Daga hagu zuwa dama: Muammar Gaddaf...
04/09/2026

Shugabannin Larabawa sun yi taro a birnin Alkahira a watan Satumba na shekarar 1970.

Daga hagu zuwa dama: Muammar Gaddafi (Libya), Yasser Arafat (Palestine), Jaafar al-Nimeiri (Sudan), Gamal Abdel Nasser (Misira/Egypt), Sarki Faisal (Saudi Arabia) da Sheikh Sabah (Kuwait).

Sun gana ne a taron kolin Kungiyar Kasashen Larabawa da aka gudanar a birnin Alkahira (Cairo) a watan Satumba na shekarar 1970. A nan ne s**a taru tare da wasu daga cikin manyan shugabannin Larabawa masu fada a ji a wancan lokaci, ciki har da Sarki Faisal na kasar Saudi Arabia, Gamal Abdel Nasser na Misira, Yasser Arafat, Muammar Gaddafi, Jaafar al-Nimeiri, da Sheikh Sabah na Kuwait.

An gudanar da taron kolin ne a lokacin wani rikici wanda Larabawa s**a korashi da suna (Black September), lokacin da fada ya barke tsakanin sojojin Jordan da Mayakan kasar Palestine (Palestinian Group).

Shugabannin na Larabawa sun gana a Alkahira (Cairo) domin tattaunawa kan tsagaita wuta da kuma hana rikicin yaduwa a fadin yankin.

Taron ya zama daya daga cikin abubuwan da Gamal Abdel Nasser yayi fitowa ta karshe a gaban jama'a a karshe. Kwanaki kadan bayan taron ya kare, ya rasu sakamakon bugun zuciya, wanda hakan ya kawo karshen mulkinsa na kusan shekaru ashirin a duniyar Larabawa.

Yau shekaru 54 kenan chif-chif da samun yancin kasar QatarYankin Qatar wanda mafi yawancin mazaunansa Musulmai ne, a huk...
03/09/2026

Yau shekaru 54 kenan chif-chif da samun yancin kasar Qatar

Yankin Qatar wanda mafi yawancin mazaunansa Musulmai ne, a hukumance ya sanar da samun cikakken 'yancin kansa daga turawan Burtaniya a daidai wannan rana, karkashin jagorancin gidan Al Thani.

Kasar mai cin gashin kanta ta karbi ragamar tafiyar da al'amuranta na cikin gida da na kasashen waje, lamarin da ya zama gagarumin sauyi a tarihin Gabas ta Tsakiya.

Address

Anaiza
00000

Opening Hours

Tuesday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rahman Yosuf posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share