Hausa Health TV

Directions

Hausa Health TV Lafiyar ka itace mafi muhimmanci a rayuwarka saboda haka, ka kula da ita da kyau

24/05/2026

Akwai abin takaici matuka yadda wasu mutane suke cin moriyar ilimin lafiya amma kuma su zama masu hana cigaban mata a wannan fanni.

Abin mamaki ne ace mutum ba ya son namiji ma’aikacin lafiya ya duba matarsa idan ta kamu da rashin lafiya, amma kuma shi kansa ba zai bari matarsa ko ‘yarsa su shiga harkar lafiya ba. Idan haka ne, wa ake so ya kula da lafiyar matanmu? Wa zai taimaka yayin haihuwa, gaggawa, ko rashin lafiya?

Wasu ma har zagi suke yi wa mata ma’aikatan lafiya, suna kiran su da sunaye marasa kyau, alhali su ne suke tsayawa dare da rana domin ceton rayukan al’umma. Wannan ba adalci ba ne. Ma’aikacin lafiya ba ya fita domin iskanci, yana fita ne domin hidima ga jama’a da ceto rayuka.

Abin tausayi ne kuma ace wasu sun auri mace saboda ilimin da ta yi, saboda mutunci da wayewar da karatu ya ba ta, amma bayan aure sai su hana ta aiki. Wannan ba soyayya ba ce, wannan tauye hakki ne da kashe burin rayuwa.
Idan muna son al’umma mai inganci, dole mu girmama ma’aikatan lafiya — mata da maza. Dole mu daina hana ‘ya’yanmu mata karatu saboda tunanin mutane. Domin yau idan babu mata ma’aikatan lafiya, mata da yawa za su shiga matsala wajen samun kulawa cikin nutsuwa da kariya.

Ku tuna: Ba za ka nemi mace ma’aikaciyar lafiya ta kula da iyalinka ba, sannan kuma ka hana naka iyalin zama ma’aikaciyar lafiya.
Allah ya shiryar da mu, ya ba mu fahimta da adalci.

Lukman Abubakar
RCHP, ND/HND Nursing in view✍️

‎Duk lokacin da aka yi maka gwajin malaria 🦟 kaga an rubuta maka NMPF a jikin katin ka, to result ɗin ka yana nufin: No ...
03/05/2026

‎Duk lokacin da aka yi maka gwajin malaria 🦟 kaga an rubuta maka NMPF a jikin katin ka, to result ɗin ka yana nufin: No Malarial Parasite Found. Shine abinda NMPF ɗin take nufi.
‎
‎✍️Idan kaga an rubuta maka: + an zagaye ta a circle, ana nufin kana ɗauke da ƙwayar halittar malarial parasite grade one ko kace early stage. A wannan stage ɗin, ƙwayar magani ma kaɗai ta ishe ka kamar irin coatem tablet preferably saboda babu buƙatar yi maka allura.
‎
‎✍️Idan kaga an rubuta maka ++ a cikin circle, ana nufin malaria ɗin ka ta kai matakin moderate ko kace intermediate wadda ana so a sanar da kai cewa zazzaɓin ka ya wuce matakin farko (yana tsakiya) amma bai kai ƙarshen malejin da ake gudu ba. Anan kana buƙatar a baka tentative strong antimalarial drugs koda ba allura bace saboda zaka iya shiga chronic stage if care is not taken. Anan stage ɗin ne mostly ake yin allurar Paluther, Chloroquine injection ko amfani da irin su Lonart ko makamantansu.
‎
‎✍️Idan kuma kaga an rubuta maka +++ a cikin circle, to result ɗin ka ya nuna cewa kana cikin tashin hankalin malarial fever wanda kana buƙatar very strong antimalarial drugs both Tablets and Injections. Anan dole ne sai ka kiyaye saboda any failure to drug treatment will be at the cost of your life. Anan ne mostly ake shan Amatem Ovul, yin allurar Emal ko kuma yin allurar Artesunate saboda ƙarfin su wajen yaƙi da malarial fever.
‎
‎A gefe guda kuma, duk lokacin da ka sha maganin malaria ko aka yi maka allura sannan ka tafi asibiti, private clinic ko wani diagnostic centre don ayi maka gwajin malaria, zai yi matuƙar wahala a iya gane akwai malaria a cikin jinin ka ko kuma babu. Wannan shine gaskiyar magana. Kasan menene dalili?, su waɗannan malarial parasites ɗin (mostly malarial falcifarum) suna ɗauke ne da wani ƙoƙo wanda suke shiga cikin sa su kwanta a lokacin daka sha maganin da zai yaƙe su. To idan ka sha wannan maganin, suna fara jin ƙanshin sa a cikin jinin ka zasu shiga cikin wannan ƙoƙon ba za'a gansu ba. Wannan ne yasa indai anyi maka gwajin malaria a lokacin da ka sha antimalarial ɗin awa 48 ko awa 24 baya kafin a ɗauki jinin naka, maganar gaskiya zai yi wahala aga ƙwayar halittar malaria a jikin ka saboda sun ɓuya cikin wannan ƙoƙon.
‎
‎Wannan ne yasa zaka ga mutum yana fama da zazzabi, amma yana zuwa Lab sai a rubuta masa NMPF. Dalilin maganin malaria ɗin da kayi amfani da shi ne kafin zuwan ka gwajin shine yasa ba za'a gansu ba koda suna nan ɗin saboda sun ɓuya cikin wannan ƙoƙon kuma sun zama capsulated ba yadda za'a yi da su. Zan baka misalin da zaka ƙara fahimtar abinda nake nufi. Kamar mutum ne ya shiga cikin gidan sa sai ya baiwa wani mukulli yace ya rufe shi ta waje. Kaga duk wanda yazo neman mai wannan gidan yaga an rufe da mukulli kai tsaye ma wucewa zai yi saboda baya buƙatar wani ƙarin bayani. Amma kuma ai mai gidan yana ciki. To wannan shine simple analogy ɗin da zan iya yi maka don ka gane abinda nake nufi.
‎
‎Note: Duk na bada misalai ne da waɗancan abubuwan don ku gane yadda abin yake. Bawai ina nufin duk abinda na faɗa ba shine exact methodology ɗin. It's just an illustrative analogy for understanding. Rubutuna na gaba akan gwajin Typhoid zan yi. ✍️
‎
‎Salisu Yakubu (RN, RNT, CT).
‎
‎Ku sauƙe wannan App ɗin wajen siyan Data mai sauƙin gaske.

Download the Strongmb app. Buy airtime, data, cable TV, electricity and more at the best prices.

02/05/2026

Kula da Lafiya wajibi ne

09/02/2026

A duk lokacin da mutum ya samu kan shi cikin wani mummunan yanayi to tabbas akwai inda matsalar take daga mutumin.

Saboda haka, kamata yayi mutum ya nemi mafita ta hanyar tsayawa ya nutsu ya fahimci inda matsalar sa take.

Ba abinda ke faruwa haka kawai ba dalili.

Idan mutum baya iya gane inda mataslar saboda yanayin damuwa ko tashin hankali da yake ciki, to ya nemi ganawa da masana halayyar ɗan-adam da Malaman addinin musulunci masu aƙida ingantacciya.

In sha Allah za'a gane inda matsalar take kuma a samu mafita.

Address

Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Health TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share